1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soke taron Sauyin yanayi a sakamakon annobar Coronavirus

Ramatu Garba Baba
May 27, 2020

Britaniya mai masaukin bakin taro kan sauyin yanayi na bana ta sanar da dage zaman taron zuwa badi bisa annobar Coronavirus da duniya ke kokarin ganin ta dakile.

https://p.dw.com/p/3cqfm
Spanien UN-Klimakonferenz 2019 COP 25 l Logo - Messe
Hoto: Reuters/S. Vera

An soke taro kan Sauyin yanayi na bana a sakamakon annobar Coronavirus, Britaniya mai masaukin bakin taron na bana ce ta sanar da hakan inda ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta dage zaman taron zuwa watan Nuwamba na shekarar badi, a watan Nuwambar bana ya kamata a gudanar da babban taron na kwanaki goma sha biyu. Ana ganin a can baya taron zai kasance mafi girma tun bayan da aka soma shi inda mahalarta za su shata sabbin matakai da zummar shawo kan barazanar da duniya ke fuskanta daga Sauyin yanayin.

Tuni dai gwmnatin Britaniyan ta aika ma Majalisar Dinkin Duniya takarda kan wannan sauyin da aka samu a taron da aka yi lakabi da COP-26. Ana fatan gudanar da taron daga ranar daya zuwa sha biyu ga watan Nuwamban shekarar ta 2021. A gobe Alhamis za a ji ko Majalisar Dinkin Duniyan za ta amince da tayin Britaniyan.