1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hajjin bana a cikin dokar nesa-nesa

July 6, 2020

Saudiyya ta sanar a wannan Litinin cewa hajjin bana zai gudana cikin tsauraran dokokin kiwon lafiya bayan da annobar coronavirus ya sa ta takaita Musulmin da za su iya sauke farali a bana.

https://p.dw.com/p/3eqDc
Saudi-Arabien Mekka | Gebet mit Social Distancing
Hoto: picture-alliance/abaca/Balkis PRess

Hukumar takaita bazuwar cututtuka ta kasar Saudiyya ta ce babu batun taba dakin Ka'aba, kuma alhazai za su rinka barin tazarar akalla mita daya da rabi a tsakaninsu. Kazalika za a takaita mutanen da za su je filin Arfa da zuwa Muzdalifah, sannan wajibi ne alhaji da sauran jami'ai su kasance sanye da takunkumi a kowane lokaci. 

Wadannan sabbin dokoki dai na zuwa ne bayan Saudiyya ta sanar da cewa mutum 1000 kawai ta amince su yi aikin hajjin. A kwanaki kuma Saudiyya ta ce ta dakatar da musulman kasashen duniya daga zuwa wannan ibada, duk dai a kokarin hana bazuwar coronavirus, wace ta addabi duniya.