Annobar Corona na ci gaba da yaduwa a sassan duniya
August 6, 2020Yawan wadanda cutar sarkewar numfashi ta Coronavirus ta kama a kasar Indiya son doshi miliyan biyu, mutum sama da dari tara ta kama a kwana guda a yayin da ta riga ta kashe wasu kimanin dubu ashirin a cikin wata guda. Ma'aikatar Lafiya a kasar ta ce akwai wasu kusan dubu dari shida da ke jinyar cutar a yanzu haka.
Annobar na ci gaba da haifar da nakassu ga manya da kananan kamfanoni, katafaren kamfanin jiragen sama na Lufthansa, ya sanar da yin asarar na Yuro biliyan daya da rabi a sakamakon takaita zirga-zirga a yayin da Kamfanin kera motoci na Toyota ya baiyana raguwar kusan dala biliyan bakwai a ribarsa, babu alamun al'amura za su iya sauya inda kamfanin ke hasashen tafka asarar a saboda annobar.
Kawo yanzu ba a kai ga samar da riga-kafin cutar ba a yayin da yawan wadanda cutar ta kama a duniya suka haura miliyan goma sha takwas tun bayan bullarta a kasar Chaina a Disambar bara.