Coronavirus za ta haddasa talauci a duniya
March 31, 2020A wani sabon rahoto da bankin duniyar ya fitar, yace ko da al'amura sun kankama, mutane kalilan ne da basu wuce muliyan 24 ba za su kaucewa fadawa kangin talauci saboda da karayar tattalin arziki da kuma tafiyar hawainiya na harkokin hada hada.
A waje guda kuma harkokin masana'antu a Chaina ya sami cigaba a watan Maris a wani abin da ya zo da ba zata yayin da harkokin kasuwanci suka koma bakin aiki bayan tsawon lokaci da suka kasance a rufe a sakamakon cutar COVID-19 wanda ya tilasta wa miliyoyin mutane zama a gida da kuma kusan tsayar da tattalin arziki.
Hannayen jari sun daga a Asia yayin da yan kasuwa suka yi maraba da bude harkokin masana'antu a China duk da cewa masana tattalin arziki na jan hankali da cewa har yanzu akwai sauran rina kaba game da matsalar tattalin arzikin duniya.