Matafiya a Afirka na fama da kalubale
February 2, 2021Ga matuka manyan motocin dakon kaya dai, shekara ta 2021 ta zo musu cikin mawuyacin yanayi na cunkoso. A yankin kudancin Afirka alal misali, akwai dokoki masu tsari kan tafiye-tafiye. A ranar 12 ga watan Janairu ne dai shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya tsaurara matakan shiga kasarsa. Har ya zuwa tsakiyar watan Fabarairu.
Ana barin motoci kalilan da ke dauke da kayan masarufi kamar abinci da magunguna da iskar gas ne kadai su tsallake kan iyaka. Hakan ya haifar da cunkoson manyan motoci a bangaren kasashen Zimbabuwe da Mozambik. A wasu lokutan, motocin kayan kan dauki tsawon kwanaki hudu kafin su ketara zuwa Afirka ta Kudu.
Wannan ba karamar illa ya ke yi wa tattalin arzikinsu ba. Wadanda ba su da izinin zama a Afrika ta Kudu na dindin, ba sa iya shiga kasar da sauki. Bugu da kari duk mai son shiga kasar sai ya rike sakamkon da ke nuni da cewar ba ya dauke da cutar corona. A ziyarar da ya kai Lemombo da ke zama kan iyakar Afirka ta Kudu da Mozambik, dan jaridar Mosambik da ke Johannesburg Milton Maluleque ya ce tsallaka iyakar babu izini abu ne mawuyaci, batun kuma da hukumomin Afirka ta Kudun suka tabbatar. Yawancin 'yan kasar Mozambik din dai, kan dauki tsawon kwanaki a wannan wuri suna neman hanyar shiga Afirka ta Kudun domin neman abun kai wa a bakin salati. Haka batun yake a kan iyakokin Kenya da Yuganda. A duk yankin gabashin Afirka dai, sai mutum na da sakamakon da ke tabbatar da cewar ba yadauke da corona kafin ya shiga wata kasa.