Sake fasalin kundin tsarin mulki a Cote d'Ivoire
March 9, 2020A cikin kundin tsarin mulkin da aka zartar a watan Oktoba na 2016 wato shekaru hudu da suka gabata, ana zaban mataimakin shugaban kasa a lokaci guda da shugaban kasa. Amma kuma wannan batu zai kau domin kuwa a cikin daftarin da gwamnatin Cote d'Ivoire za ta mika wa 'yan majalisar dokoki da na dattijai, shugaban kasa ne zai nada wadanda ya ga dama a wannan mukami na mataimakin shugaban kasa, bisa amincewar majalisar. Wannan ne ma babban sauyi da za a samu a sabon kundin tsarin mulkin kasar, lamarin da Sylvain Nguessan, manazarcin harkokin siyasa ya yi na'am da shi duba da zubin shugabancin Cote d'Ivoire.
"Ouattara, a matsayinsa na shugaban kasa, ya auna tasirin wannan mataki kafin ya yanke duk wadannan hukunce-hukunce. Babu shakka ya ga cewa zai fi kyau shugaban da aka zaba ya samu damar nada mataimakinsa. A kasar Cote d'Ivoire, inda Firaminista ya fi mataimakin shugaban kasa karfin iko, shugaban kasa ne ke nada shi. Don haka babu wani abin da zai hana shi nada mataimakinsa."
Sai dai kuma duk da kin yin tazarce domin bai wa masu karancin shekaru bada tasu gudunmawa a kasar, amma kuma shugaba Ouattara bai rage yawan shekaru da ya kamata 'yan kasa su kai kafin su tsaya takarar shugabancin kasa ba. A wannan marra dai babu wani canji, dole ne mutum ya mari akalla shekaru 35 da haihuwa imma mace koko namiji.
A fannin shari'a kuwa, daftarin sake fasalin tsarin mulki da za a gabatar wa majalisu biyu na kasar ya tanadi soke kotun koli, inda za a madadinta za a kafa wasu kotuna biyu, daya da ke bada matsayi kan duk abubuwan da suka shafi kundin tsarin mulki da kuma wacce za ta kula da kararrakin da aka daukaka.
Wani batu mai muhimmanci da za a sake fasalinsa cikin tsarin mulkin kasar ta Cote d'Ivoire shi ne na aikin majalisun dokoki da na dattawa: ma'ana daga yanzu idan bisa ga wasu hujjoji ba zai yiwu a gudanar da zabukan 'yan majalisar a kan lokaci ba, majalisar da ke ci za ta ci gaba da aikinta har sai an gudanar da zabuka masu zuwa.
Sai dai wadannan sauye-sauye sun yi hannun riga da bukatun 'yan adawa, a cewar tsohuwar minista Danielle Boni Claverie, da ke da kusanci da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo.
"Muna mai da hankali kan hanyoyin inganta yanayin shirya zabuka masu zuwa don su kasance an gudanar da su cikin gaskiya kuma ba tare da jayayya ba. Muna kuma mai da hankali sosai kan abin da zai faru a ranar 12 ga watan Maris a gaban kotun kare hakkin dan Adam ta Afirka kan takaddamar da ke tsakaninmu da gwamnatin Cote d'Ivoire kan samar da cikakken 'yancin gudanar da aiki a CEI, Hukumar Zabe."
Dama baya ga sake fasalin kundin tsarin mulki, 'yan majalisar wakilai da sanatocin kasar za su kada kuri'a kan kudirin doka da ya shafi ka'idojin takara da samun tallafi a babban zabe da zai gudana cikin watanni masu zuwa. Bisa ga sakamakon tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa dai, sai idan mutum ya samu amincewar kashi daya cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri'a ne zai iya tsayawa takarar shugaban kasa, sannan kuma za a kara kudade da kowanne dan takara ya kamata ya zuba daga miliyan 20 zuwa miliyan 50 na CFA a zaben shugaban kasa. A karshe kuma za a tanadi mayar wa duk dan takarar da ya samu akalla kashi 5 cikin 100 na kuri'un da aka kada kudin da ya zuba. 'Yan majalisun dokoki da na dattawan Cote d'Ivoire za su shafe tsawon watan Maris suna muhawara da gyare-gyaren fuska kafin su kada kuri'ar amincewa da gyaran fuska da suka yi wa kundin na tsarin mulkin.