Cote d'Ivoire: Watsi da takarar Gbagbo
June 30, 2023Talla
A sanarwar da jam'iyyarsa ta PPA-CI ta fidda a wannan Jumma'a ta ce hukumar zaben ta kafa hujja da cewa tsohon shugaban na fuskantar tuhuma ta hukuncin daurin shekaru 20 a Cote d'Ivoire duk kuwa da wanke shi da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta yi a watan Maris na 2021.
Jam'iyyar tsohon shugaban kasar ta alakanta wannan mataki da bita da kulli da shugaba mai ci Alassane Ouattara ke yi wa Gbagbo, kana kuma ta ce wannan neman sarewa magoyan bayanta guwiwa ne yayin da zaben kananan hukumomin kasar ke karatowa.
Daga nasa waje shugaba Laurent Gbagbo ya ce zai ci gaba da gwagwarmaya har sai hakar ta cimma ruwa domin ba bu gaskiya a duk tuhume-tuhume da hukumar ta zano a kansa.