1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanda suka mutu da coronavirus sun haura a duniya

Abdoulaye Mamane Amadou
May 12, 2020

Yawan wadanda annobar Covid-19 ta halaka sun haura dubu 284 a yayin da wadanda suka kamu da cutar suka kai miliyan hudu da digo 14 a duniya a daidai lokacin da kasashe ke sassauta dokar kulle.

https://p.dw.com/p/3c3vR
New York Coronavirus Leichenabstransport
Hoto: Getty Images/AFP/B. Smith

Har yanzu Amirka ce ke kan gaba da wadanda suka fi mutuwa da cutar, inda alkaluma suka ce mutun 80.000 ne suka kwanta dama bisa kamuwa da corona, Birtaniya na biye mata da mamata 32.065, sai Italiya mai mamata 26.744 a yayin da Faransa ke da mamata 26.643.

Tuni dai kasashe irin su Faransa da Spain da Holand da Beljiyam da Ukrain suka bayyana matakan sassauta dokokin kulle, a yayin da Birtaniya ta tsawaita matakin har zuwa ranar daya da watan Yuni.

Shugaba Vladimir Poutine na kasar Rasha, ya bayyana dage dokar kullen kasar a yayin da ya mika jan ragamar tafiyar da tsarin ga yankunan kasar.