Wadanda suka mutu da coronavirus sun karu
May 22, 2020Talla
An lura da samun karuwar mutuwar jama'ar da suka kamu da cutar a baya bayan nan a yankin Latin Amirka, inda a kasar Brazil kawai mamata suka zarta fiye da mutun dubu 20 000 da suka mutu da cutar. Har yanzu Amirka ita ce ke kan gaba daga cikin jerin kasashen da cutar ta yi wa mummunar barna, inda take da mamata 94.661. Birtaniya na da mamata 36.042. Italiya 32.486. Faransa 28.215, sai Spain 27.940. Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce yana sanya takunkumin fuska lokaci zuwa lokaci idan har bukatar hakan ta taso, to amma sai dai yana guje sanyashi a gaban 'yan jarida, sai kalamun shuigaban na zuwa ne a daidai lokacin da ya bayar da umarnin sasauto tutocin kasar domin nuna jimami ga wadanda suka rasa ransu da cutar ta corona a kasar.