1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-19: Alkaluman wanda suka rasu a Iran

Ahmed Salisu
February 24, 2020

Rahotannin daga yankin nan na Qom a kasar Iran na cewar yawan wadanda suka kamu da cutar nan ta Coronavirus ko Covid-19 ya karu inda yanzu haka adadin ya kai mutum 50.

https://p.dw.com/p/3YI7f
Coronavirus
Hoto: picture-alliance/AP/NIAID-RML

Dan majalisa da ke wakiltar yankin na Qom a majalisar dokokin Iran din ne ya ambata hakan a wannan Litinin din, sai dai alkaluman da ya bada sun ci karo da wanda ma'aiakar kiwon lafiya ta kasar ta bada a yau din.

Mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar Iran din Iraj Haririci ya ce baya ga jami'an kiwon alfiya, ba wanda ke da hakikanin alkaluma na wadanda cutar ta halaka, inda a share guda ya ce a hukumance mutum 12 ne suka tabbatar da rasuwarsu yayin da wasu 61 yanzu haka ke dauke da cutar.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da hukumomin Italiya suka bada sanarwar cewar ya zuwa yanzu cutar ta Covid-19 ta yi sanadin hallaka mutum 5 yayin da Koriya Kudu kuwa ta bada sanarwar cewar ya an samu karin mutum 231 da suka kamu da wannan cuta.