Shugabannin kasashe sun halarci taro kan cutar COVID-19
May 4, 2020Talla
An gabatar da wannan bukata ne yayin babban taron da ya gudana ta bidiyo a wannan Litinin din, wanda kungiyar EU ta shirya. a lokacin wannan taro dai babu wakilcin kasashen Amirka da Rasha duk kuwa da cewar annobar ta Covid-19 tayi sanadiyyar mutuwar mutanen da yawansu ya kai 67,000 a Amirka .
Da yake jawabi a lokacin taron babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya jaddada muhimmancin hadin kai da bukatar yin watsi da gasa a wannan lokaci na laluben rigakafin COVID-19, bayan ya jaddada bukatar amfani da kudaden a bangaren samar da rigakafin da kuma gudanar da sabbin gwaje-gwaje.