1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sake bude wuraren ibada

Mahaman Kanta LMJ
May 13, 2020

A Jamhuriyar Nijar gwamnati ta dage dokar rufe wuraren ibada wacce ta sanya a karshen watan Maris, a wani mataki na dakile yaduwar annobar cutar coronavirus a kasar.

https://p.dw.com/p/3cAL3
Niger Moschee in Niamey
An bude wuraren ibada a NijarHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a daren ranar talatar da ta gabata, ta ce ta dauki matakin bude wuraren ibadar wanda zai fara aiki daga wannan Larabar a fadin kasar ne, sakamakon shawarar shugabannin addinai na kasar. Mahukuntan na Nijar sun bayyana cewa, haka kuma sun ji ta bakin kwamitin kwararru da ke yaki da cutar ta COVID-19 na kasar, dangane da yadda annobar ta fara ja da baya.

Sai dai gwamnatin ta yi kira ga shugabannin addinai da su dauki matakai na kiyayewa da suka hadar da feshin magani a wuraren ibadar bayan kowace salla da saka takunkumi da kuma barin tazara ta akalla mita daya tsakanin mahalarta wurin ibadar da kuma wanke hannuwa da sabulu kafin shiga wuraren ibadar. Kazalika gwamnatin ta dage dokar hana yawon dare a birnin Yamai daga wannan Larabar.

Sai dai gwamnatin ta yi gargadin yiwuwar sake dawo da dokar idan aka sake fuskantar matsalar annobar. Masu rajin kare hakkin dan Adam da matasa da ke yin wasu sana'o'i da daddare, sun yi maraba da matakin dage dokar hana fita da daddaren da mahkuntan suka sanya. Tunima dai Masallatai a Jamhuriyar ta Nijar suka fara gabatar da sallolin jam'i, kamar yadda aka saba a baya kafin shigowar annobar ta coronavirus.