1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Corona ta yi kamari a Jamus

Abdullahi Tanko Bala
November 19, 2021

Ministan lafiya na Jamus Jens Spahn ya ce annobar Corona ta yi kamari inda a yanzu kasar ke fuskantar yanayi na dokar ta baci.

https://p.dw.com/p/43H21
Herrsching Am Ammersee | Coronavirus - Intensivtransport
Hoto: Matthias Balk/dpa/picture alliance

Da yake jawabi ga 'yan jarida ministan lafiyar Jens Spahn a halin da ake ciki ba a fidda tsammanin sake dawo da dokar kulle idan ta kama domin shawo kan yaduwar cutar a fadin kasar.

Kalaman ministan na zuwa ne yayin da majalisar dattijai ta Bundestag ta amince da daukar sabbin matakai na dakile cutar ta corona kwana guda bayan da majalisar wakilai itama ta zartar da daukar matakin.

A waje guda kuma Jihar Bavaria da ke kudu maso gabashin Jamus a wannan Juma'ar ta soke gudanar da kasuwar Kirsimeti ta bana a wani mataki na dakile yaduwar cutar corona.

Firimiyan jihar Markus Soeder ya shaidawa taron manema labarai cewa an rufe dukkan gidajen rawa da wuraren sayar da barasa da kuma wuraren sayar da abinci da ke budewa da dare domin shawo kan barkewar annobar karo na hudu.