Masu maganin gargajiya da COVID-19
April 7, 2020Duk da yake ya zuwa yanzu ba a kai ga tabbatar da samun maganin riga kafin cutar ta COVID-19 ba, fargabar kamuwa da cutar da jama'a suke da ita na sa mafi yawansu na amfani da magungunan gargajiya a Kamaru, wannan kuwa duk da illolin da haduran da ke tattare da hakan. Ana iya cewa dai jimawar da aka yi ba tare da samun wani magani da ka iya yin garkuwa ko riga kafin kamuwa da cutar Coronavirus ba, na daya daga cikin abubuwan da ke kara taimakawa wajen yaduwar magunguna kala-kala irin na gargajiya a shafukan Internet.
Kasuwar magungunan gargajiya
Dr Abanké kamar yadda ake kiransa na zaman guda dga cikin wadanda suka kira kansu masu bayar da magani na kamuwa da cutar ta covid-19 da ke cewa yana bayar da ke kara garkuwar jiki yana mai cewa za su hana mutum kamuwa da cututtuka, kasancewar cuta na shiga jikin mutum ne sakamakon karancin garkuwar jikin.
Kamar Dr Abanke dai mutane da dama ne ke tallata magungunansu irin na gargajiya a shafukan sada zumunta na Intanet, da suke ikirarin cewa suna iya bayar da maganin Coronavirus din.
Illar shan magani barkatai
Marie Marie Cécile na amfni da hade-haden na gargajiya ta kuma ce idan har an ce wadannan jike-jiken na iya warkar da duk wata cuta ta huhu ko mura da dangoginsu, to za su iya warkar da Coronavirus. Amfani da magunguna da jike-jiken ko yin surace da itatuwan gargajiya ya zarta kima, kana kuma sayen magunguna na asibitoci a gidajen sayar da magani ba tare da shawarar likita ba shi ma ya karu, tun lokacin da cutar ta Coronavirus ta bullu a kasar Kamaru.