1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta dage dokar killacewar corona

Abdullahi Tanko Bala
May 15, 2020

Nan gaba kadan duk wanda ya shigo Jamus ko mazaunin da ya dawo kasar daga ketare ba za a killace shi dole ba.

https://p.dw.com/p/3cJ7G
Forderungen nach Wiederöffnung der EU-Grenzen wachsen mit Lockdown-Maßnahmen
Hoto: Getty Images/T. Niedermueller

Nan gaba kadan duk wanda ya shigo Jamus ko mazaunin da ya dawo kasar daga ketare ba za a killace shi a dole ba, sai dai zai zaman kulle a gida tsawon kwanaki 14. Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin tarayyar Jamus da takwarorinta na jihohin kasar suka amince da shi bayan amincewa da janye matakan bincike a kan iyakokin kasar.

A cikin kwanaki masu zuwa za a sanya ka'idojin a cikin kundin dokokin jihohin kasar a cewar ma'aikatar cikin gidan Jamus.

Masu shigowa kasar daga kasashen kungiyar tarayyar Turai da na Schengen da kuma kasar Birtaniya za su yi aiki da shawarar kulle kansu a gida tsawon kwanaki 14, idan sun fito daga kasashen da ke da babbar kasada ta yaduwar annobar corona.