1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar Corona na kamari a Indiya

Abdoulaye Mamane Amadou
December 19, 2020

Annobar Covid-19 na ci gaba da daukar hankalin kasashen duniya, a daidai lokacin da mutane miliyan 10 suka kamu da cutar a kasar Indiya, Italiya na shirin tsunduma cikin dokar kulle.

https://p.dw.com/p/3mwtc
Indien I Coronavirus I Mitarbeiter des Gesundheitssystems in Mumbai
Hoto: Reuters/A. Dave

Kasar Indiya ita ce ta biyu a duniya da cutar corona ta fi yawan yaduwa, inda mutun miliyan 10 ke dauke da ita a yanzu, kamar yadda alkaluman da ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta fitar suka tabbatar. Rahotanni na cewa kasar ta samu fiye da mutun dubu 25 da suka kamu da annobar ta Covid-19 a cikin kwana guda.

Italiya za ta sake shiga dokar kulle har zuwa karshen bukuwan Kirsimeti daga ranar Litinin 21 ga watan Disamba, biyo bayan samun adadin wadanda suka mutu da cutar corona fiye da dubu 68 a ranar Juma'a.

Hukumar FDA ta Amirka ta amince da soma aiki da allurar rigakafin nan na Moderna a wani yunkuri na dakilye yaduwar annobar corona da ke ci gaba da daukar rayukan jama'a.