1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Raguwar angizo kan yaki da annoba

Abdullahi Tanko Bala
July 25, 2020

Binciken jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a wasu kasashe shidda ya nuna jama'a basu gamsu da matakan da gwamnatoci ke dauka na shawo kan annoba da ta shafi lafiya ba.

https://p.dw.com/p/3fuhC
Deutschland Berlin Mund-Nasen-Maske Mundschutz
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Sohn

Mutane da dama da aka ji ra'ayoyinsu sun baiyana cewa sun yi imani mutane da dama na mutuwa fiye da alkaluman da ake baiyanawa a hukumance.

A halin da ake ciki Jamus na kokarin magance matsalolin da suka taso game da manhajar bin diddigi don gano masu dauke da kwayar cutar corona.

An baiyana cewa manhajar ta Andriod da ake amfani da ita wajen tantancewar bata aiki yadda ya kamata.

Gwamnan jihar Saxony Michael Kretschmer yace ya yi amanna tuni aka shiga zango na biyu na annobar corona a Jamus.