Senegal cin galabar COVID-19
May 12, 2020Talla
Shugaba kasar ta Senegal Macky Sall shi ne ya bayar da wannan sanarwar tare da sassauta dokar hana zirga-zirga da aka kakaba domin yaki da annobar Corona.
Kasar ta Senegal na kan gaba cikin kasashen duniya da suka ci karfin annobar ta coronavirus da ta kama mutane 1886 a kasar, inda tuni 715 suka murmure daga cutar, kana mutune 19 ne suka mutu bayan kamuwa da cutar.
A wani yunkuri na baya-bayan nan, kasar ta fara gwajin na'urorin gwajin cutar cikin mintoci 10, kuma masu saukin kudi da mutum zai iya gwada kansa daga gida. Haka zalika gwamnatin Senegal ta amince a gwada maganin gargajiya da aka samu a kasar Madagaska.