1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Yara 10,000 na mutuwa a kowane wata

July 28, 2020

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla kananan yara 10,000 ke mutuwa a kowane wata a duniya a sakamakon yunwa da annobar corona ke haddasawa.

https://p.dw.com/p/3g1Im
Nordkorea - Hungersnot
Hoto: picture-alliance/AP Photo/World Food Program/S. Buhr

Majalisar ta ce kananan yara na fusakantar matsananciyar yunwa a saboda yadda matakan kariya daga corona suka sanya manyan gidajen gona ba sa iya kai kayansu kasuwanni. Haka kuma majalisar ta ce akwai wasu kauyuka da tasirin annobar ya kawo musu tangarda wurin samun abinci da magungunan da ake shigo musu da su daga birane.

Francesco Branca jami'in da ke kula da samar da ingantaccen abinci a hukumar lafiya ta duniya ya ce yana zullumin abin da ake gani yanzu kamar somin tabi ne idan aka dubi tasirin da corona ke yi wurin samar da cimaka a duniya. Majalisar Dinkin Duniyar ta ce wannan matsala tafi kamari a yankunan da ke fama da talauci.