Cuta mai kama da Ebola ta bulla a Yuganda
October 19, 2017Talla
Kasar Yuganda ta tabbatar da samuwar mutum guda da ya harbu da kwayoyin cutar Marburg, cutar da ke haifar da zazzabi mai zafi mai kama da na cutar Ebola wacce kuma ke saurin bazuwa kamar yadda ma'aikatar lafiyar kasar ta bayyana a wannan Alhamis.
Jane Ruth Aceng ministar lafiya a Yuganda ta fadawa manema labarai cewa an tabbatar da samuwar mutum da ya harbu da kwayoyin cutar ta Marburg mai kama da Ebola bayan lokaci da aka dauka ana zurfafa bincike, sai dai ba ta kara cewa komai ba baya ga wannan.
Kasar da ke a Gabashin Afirka ta samu bullar annobar cutar ta Marburg a shekarar 2014, kuma kwayoyin wannan cuta sun fito ne daga iyalan Ebola wacce a shekarar 2014 ta halaka mutane dubbai.