Cutar Ebola ta bulla a kasar Senegal
August 29, 2014Ministan kiwon lafiyar kasar ta Senegal Awa Marie Coll Seck shi ne ya tabbatar da hakan a wani jawabi da ya yi ga manema labarai dazu inda ya ke cewar wanda ya kamu din wani matashi ne da ya koma kasar daga Gini.
Bullar cutar a Senegal dai na zuwa bayan da Kungiyar Lafiya ta Duniya ta ce yawan wadanda suka kamu da cutar a yammacin Afirka a makon da ya gabata shi ne mafi muni tun bayan da cutar ta bayyana a yankin.
A wani karin haske da ta yi dazu, kungiyar ta ce mutane sama da dari biyar ne suka kamu a makon da ya gabata kadai kuma galibinsu a kasar Liberiya ne ko da dai ta ce an samu karuwar masu dauke da cutar a kasashen Gini da Saliyo.
Kimanin mutane 1500 ne yanzu haka aka bada labarin rasuwarsu tun bayan da cutar ta bayyana a Afirka ta yamma kuma a jiya Alhamis Kungiyar Lafiyar ta Duniya ta ce alamu na nuna cewa mutane dubu 20 na iya kamu da cutar kafin a kai ga shawo kanta duba da yadda ta ke bazuwa cikin sauri.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman