1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maleriya na barazana ga mata da yara

Abdul-raheem Hassan
December 4, 2019

Sabon rahoton hukumar lafiya ta duniya ya nunar cewa maleriya na kashe sama da mutane dubu 400 a kowace shekara saboda rashin tallafin yaki da cutar. WHO ya ce rabin al'ummar duniya na cikin hatsarin kamuwa da cutar.

https://p.dw.com/p/3UB8F
Symbolbild Treffen Geberländer Globaler Fonds zur Bekämpfung von Aids,Tuberkulose und Malaria
Hoto: picture-alliance/dpa/Keystone/G. Bally

Miliyoyin mutane na kamuwa da cutar maleriya musamman kananan yara da mata masu juna biyu a kasashen Afirka. Rahoton ya nuna takaicin yadda cutar maleriyar ke ci gaba da zama barazana sakamakon jan kafa na samun kudaden yaki da cutar baki daya.

Sabon rahoton na WHO ya ce an samu raguwar hatsarin kamuwa da cutar a 2018 idan aka kwatanta da 2017, amma duk da haka hukumar ta kiraye kasashen da cutar ta fi kamari da su dage wajen maganceta.