1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Numoniya ta yi kisa fiye da maleriya a 2018

Gazali Abdou Tasawa
November 12, 2019

Asusun Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya, Unicef ta bayyana damuwarta dangane da yadda cutar nomoniya ke ci gaba da kisan kananan yara a duniya inda take halaka yaro daya a kowane sakon 39.

https://p.dw.com/p/3SrXc
Symbolbild | Frühgeborenes | Frühchen
Hoto: picture-alliance/dpa/ZB/W. Grubitzsch

Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya Unicef ta bayyana wannan damuwa ce a wannan Talata da ke zama ranar da MDD ta ware domin yaki da wannan cuta.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da hukumar ta Unicef da wasu kungiyoyin biyar masu fafutikar kare lafiyar kananan yara da suka hada da Save The Children suka fitar sun bayyana cewa a shekarar da ta gabata cutar ta numoniya da ke haddasa matsalar sheda ta halaka yara 'yan kasa da shekaru biyar sama da dubu 800 a duniya daga cikinsu kusan dubu 153 kafin su yi wata daya a duniya.

 Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ko OMS ta ce cutar numoniya na zaman dalilin mutuwar kaso 15 cikin dari na yara 'yan kasa da shekaru biyar a duniya musamman a kasashen Najeriya, Indiya, Pakistan, Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, da Habasha. kuma cutar ta kashe yara fiye da malaeriya a shekara ta 2018.