Cutar Zika na kara bazuwa a Kwalambiya
February 6, 2016Talla
Wasu sabbin alkaluma da hukumomin kiwon lafiya na kasar Kwalambiya suka fitar a wannan Asabar sun nunar da cewa adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da kwayar cutar Zika ya kai mutun sama da dubu 22 da 600 daga cikin kimanin dubu 26 da ake zargin sun kamu da cutar a fadin kasar.
Alkaluman sun kuma nunar da cewa kashi 64 da digo takwas daga cikin dari na mutanen da suka kamu da cutar mata ne, daga cikinsu kuma dubu biyu da 824 masu juna biyu.
Haka zalika hukumomin kasar Kwalanbiyar sun tabbatar da mutuwar mutane uku kawo yanzu daga cikin wadanda ake zargi da kamuwa da kwayar cutar ta Zika wacce ke haddasa haifar jarirrai da dan karamin kai da ke yin munmunan tasiri ga hankali dama iliminsu.