Tattalin arzikin Côte d'Ivoire ya shiga wani hali
June 16, 2020Talla
Sanarwar gwamnatin kasar ta ce tana son ta yi amfani da kudin da take da su a hannunta wurin inganta asibitocin kasar don tunkarar annobar coronavirus. Kazalika idan har kasashen suka tsahirta mata biyan bashin, za ta yi amfani da dukiyar wurin bunkasa tattalin arzikin kasar wanda corona ta kassara.
Sanarwar gwamnatin ta ce tuni kasar ta Côte d'Ivoire ta tura wa kasashen da ke binta bashi wannan roko a hukumance, inda take son a daga mata kafar ci gaba da biyan bashin akalla dala milyan 205.