1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

Daftarin taron Masar

Suleiman Babayo AH
November 17, 2022

Akwai yuwuwar samun sabani tsakanin kasashe yayin da aka fara rubuta daftarin taron saunyin yanayi da ke gudana a kasra Masar.

https://p.dw.com/p/4Jg8K
Masu zanga-zanga a wajen taron kare muhalli a Masar
Taron kare muhalli a MasarHoto: MOHAMMED ABED/AFP

An fara rubuta daftarin taron kare muhalli na COP27 da ke wakana a kasar Masar kan sauyin yanayi inda ake fatan ganin dumamar duniya bai fi maki 1.5 a ma'aunin zafi, amma akwai wasu wurare da ake ganin za a iya samun sabani tsakanin kasashen duniya.

A wannan Jumma'a ake kawo karshen taron mai yuwuwa ba tare da samun duk kasashen sun amince da matsayi guda ba. Akwai yuwuwar samun kalamai ba masu sassauci, musamman kan ci gaba da amfani da man fetur maimakon makamashin da ake sabuntawa. Sai dai tun farkon wannan makon kasashen Amirka da China da suke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya kuma na gaba wajen fitar da iskar da ke gurbata muhalli sun amince da aiki tare.