Daga Bush zuwa Biden: Alakar Merkel da shugabannin Amirka
Tun bayan da Angela Merkel ta zama shugabar gwamnatin Jamus shekaru sama 15 baya, ta yi zamani da shugabannin Amirka uku. Bayan tsamin danganta da mulkin Trump an ga canji a zamanin Joe Biden.
Kallon kallo
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban Amirka Donald Trump na da bambancin ra'ayi kan kasar Iran da harkar kasuwanci da kungiyar NATO da sauransu. Amma sabanin ra'ayin ya yi tsanani har ta kai ga Trump ya kira Merkel "wawiya" a taron NATO a 2019. Shugabannin suna wa juna kallon hadarin kaji.
Waye shugaba?
Hoton da ya tayar da kura a duniya: Mekel da Trump yayin taron G7 a Kanada, cikin watan Yunin 2018. Merkel ce ke da iko yayin da take tsaye a gaban Trump? Ko dai Trump da ke zaune? Hukumomin Jamus ne suka fitar da hoton dauke da taken "taron ba zata tsakanin manya biyu."
Haduwa ba musabaha
Shugaba Trump ya bayyana a tsaye lokacin da ya karbi bakwancin Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a Fadar White House a watan Maris na 2017. Shugaban na Amirka ya ki mika hannu ga Merkel a gaban manema labarai. Hoton ya bayyana tsamin dangantaka a haduwarsu ta farko.
Kallo cikin kwayar ido
Dangantakar Merkel da Barack Obama ta kasance dabam da ta Trump. Merkel da Obama sun zama kamar abokai tsawon wa'adin shugabancinsa na shekaru takwas a Amirka. An dauki wannan hoto a watan Nuwamban shekarar 2016, lokacin da Obama ya je ziyarar bankwana a Berlin, 'yan kwanaki kadan bayan zabar Donald Trump a matsayin wanda zai gaje shi.
Ado da murmushi
A watan Yunin 2011, Merkel ta karbi lambar girmamawa ta shugaban kasa kan ‘yanci, babbar lambar yabo ta farar hula a Amirka. Obama ya yaba da jajircewarta ga hadin kan Turai. Masu sa ido sun danganta kyautar a matsayin tabbacin kyakkyawar dangantakar kasashen Jamus da Amirka.
Lokacin kulla abota
Merkel da Obama sun samu daidaito a taron G7 a tsaunin Bavariya a shekarar 2015. Shugabar gwamnatin ta iya dogaro da goyon bayan Amirka a kan batutuwa da dama, kamar na yaki da sauyin yanayi. Sai dai lamarin ya wargaje ba shiri lokacin da Trump ya zama shugaban Amirka a 2016.
Kana ji kamar yadda nake ji?
A ganawarsu ta farko a watan Yulin 2006, wanda Obama ya gada George W. Bush ya yaba kan yadda Merkel ke son 'yancin walwala. A taron G8 da aka yi a St. Petersburg a watan Yulin 2006 ya mata tausar ba zata a wuya, amma duk da haka bai haddasa baraka a dangantakarsu ba.
Siyasar cin naman alade
A watan Yulin 2006, Bush ya ji dadin sanya gasashshen nama a farantin Merkel yayin da ta kar bakuncinsa a mazabarta da ke gabar tekun jiharta a Arewa maso Gabashin Jamus wato Mecklenburg. Gashin nama shi ya fi daukar hankali a ziyarar da aka kai wa Merkel garinta.
Nan yankina ne
A shekarar 2007 Merkel ta ziyarci Bush a gonar kiwo a Texas. Bush da kansa ya yi wa Merkel da mijinta Joachim Sauer kwalliya a cikin babbar motar daukar kaya ta Amirka. Merkel da Bush sun amince su yi aiki tare don nemo hanyar diflomasiyya kan rikicin makamashin nukiliyar Iran.
Dangantakar Turai da Amirka
A wajen taron jana'izar tsohon Shugaban gwamnatin Jamus Helmut Kohl a watan Yulin 2017, tsohon shugaban kasar Amirka, Bill Clinton ya gabatar da kalaman ban dariya da tausayawa. "Na kaunace shi," in ji shi. Lokacin da ya sake zama, sai ya kama hannun Merkel.
Yaba kyauta tukuici
A watan Nuwambar shekara ta 2009: Merkel ta gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin Amirka a birnin Washington DC. Yayin da take shan tafi, mataimakin shugaban kasa na lokacin Joe Biden ya nishadantar da shugabar har ta yi dariya. Fatan alheri ga kawancen Jamus da Amirka. Yanzu an zabi Biden a matsayin shugaban kasa.