Najeriya: Babban zabe ya mamaye jaridun Jamus.
February 22, 2019Dage babban zabe da mako guda da hukumar zabe mai zama kanta a Najeriya wato INEC, ta yi ya dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.
A labarin da ta buga jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce matakin da hukumar ta INEC ta dauka jim kadan da a fara kada kuri'a ya fusata 'yan Najeriya da dama kasancewa wasunsu sun yi tafiya zuwa yankunansu masu nisa don sauke wannan nauyi, yanzu haka ma da dama a cewa ba za su sake yin wannan tafiya saboda zaben ba, inda bisa ga dukkan alamu za a yi kankankan tsakanin shugaba mai ci Muhammadu Buhari na APC da dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar. Jaridar ta ce ban da fusata jama'a da dage zaben ya yi da kuma illar da ya yi wa sunan kasar musamman tsakanin masu zuba jari, matakin ya tabbatar da matsalar cin hanci da halin rashin tabbas da kasar ke ciki. INEC ta ce rashin isar kayakinzabe a wasu sassa na kasar na daga cikin dalilan da suam sanya ta dage zaben.
Dage babban zaben Najeriya ya janyo babbar asara fanin tattalin arziki kamar yada kwararru suka nunar
Ita ma a sharhinta dangane da zaben na Najeriya jaridar die Tageszeitung ta ce sake ranar gudanar da zaben ya dagula al'amura a Najeriya. Jaridar ta ruwaito masana tattalin arziki a Najeriya na kwatanta irin asarar da dage zabe ya janyo da aka kiyasta ta kai Euro miliyan 341. Jaridar ta ce abin da ya fi muni shi ne rashin yarda da wannan matakin ya janyo wa hukumar zaben kasar wato INEC. Yanzu ya zame wa hukumar INEC wajibi ta shirya ta kuma gudanar da zaben da zai samu karbuwa ga dukkan 'yan Najeriya.
Rashin wutar lantarki a Afirka ta Kudu ya janyo koma baya na tattalin arziki a kasar baki daya
Kasar Afirka ta Kudu na fama da matsalar daukewar hsken wutar lantarki inji jaridar Neueu Zürcher Zeitung tana mai cewa tattalin arzikin Afirka ta Kudu ya shiga mawuyacin hali sakamakon matsalar ta wutar lantarki inda yanzu haka kamfanin makamashi na kasar wato Eskom ke bukatar taimako. Jaridar ta ce rashin iya gudanar da aiki da almundahana da uwa uba matsalar cin hanci da rashawa sune musabbabin wannan hali na yawan daukewar hasken wutar lantarki a Afirka ta Kudu. A tsakiyar wannan mako an jiyo sabon ministan kudi Tito Mboweni na cewa gwamnati za ta taimaka wa kamfanin da kudi miliyan dubu 23 na Rand a tsukin shekaru uku amma karkashin tsauraran sharudda ciki har da yi wa kamfanin na Eskom kwaskwarima da sayar da wani bangresa ga 'yan kasuwa masu zaman kansu.
A karshe sai jaridar sai jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta ruwaito shugabannin Cibiyar zuba jari da raya kasa ta Jamus wato DEG da ke zama reshen na Bankin ba da bashi don raya kasa na KfW na cewa sun amince da bai wa kamfanoni masu zuba jari a kasashe masu tasowa Euro miliyan dubu 1.9 wato karin miliyan 300 idan aka kwatanta da na bara. Cibiyar ta ce musamman za ta fi mayar da hankali a Afirka ta ce buri shi ne tallafa wa bunkasar aikin kamfanoni da sama wa matasa kyakkyawar makoma musamman a fannin koyan sana'o'i.