Kare rijioyin mai daga shiga hannu IS a Siriya
October 21, 2019Amirka ta ci gaba da janye dakarunta daga kasar Siriya, wani ayarin motocin sojojin ya tsallake kan iyaka zuwa Iraki, a wani abin da tashar telebijin ta CNN ta ruwaito wani jami'in Amirka na cewa shi ne matakin sake tsugunar da sojojin Amirka mafi girma a yankin.
A ranar Asabar an jiyo sakataren tsaron Amirka Mark Esper na cewa sojoji kimanin dubu daya daga arewacin Siriyar ake sa ran isarsu kasar Iraki.
Sai dai kuma yayin da yake magana lokacin ziyarar da yake kaiwa a kasar Afghanistan Esper ya ce ana tattauna batun yiwuwar barin wasu dakarun Amirka a Arewa maso Gabashin Siriya kusa da wasu rijiyoyin mai don ganin rijioyin na mai ba su fada hannun mayakan IS ba.
"Muna da dakaru a Kudu da Arewa maso Gabashin Siriya da muka girke kusa da rijiyoyin mai. Wadannan dakaru da ke a garuruwan ba sa cikin wadanda muke janyewa a yanzu. Kamar yadda na fada aikin zai dauki tsawon makonni, kafin lokacin dakarunmu za su ci gaba da zama a garuruwan na kusa da rijiyoyin man."