Dakarun Siriya sun zafafa kai hari
January 3, 2017Talla
Bisa dukkan alamu yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin kasar Siriya na fuskantar barazana, sakamakon zafafa kai hare hare da dakarun gwamnati ke yi kusa da birnin Damaskus. Tuni dai wasu kungiyoyin 'yan tawaye wajen 10 suka ayyana manufarsu na dakatar da shiga tattaunawar sulhu da ake shirin gudanarwa a wannan wata.
Ana shirin komawa teburin sulhu a babban birnin Kazakh watau Astana a karshen wannan wata na Janairu, sai dai 'yan tawayen sun ce za su janye ne saboda abun da suka kira "watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki hudu da Damaskus ta yi".
Rasha ce dai ta ke shirya gudanar da zaman sulhun tare da tallafin gwamnatin Siriya, a daya hannun kuma da Turkiyya da Iran da ke goyon bayan 'yan tawayen kasar.