1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun sojan Ukraine 568 suka mutu

August 11, 2014

Sojojin Ukraine sama da dari biyar ne suka halaka a fafatawar da su ke da 'yan aware dake samun goyon bayan kasar Rasha, a cewar majiyar jamian sojan kasar.

https://p.dw.com/p/1CsaV
Konvoi russischer Militärfahrzeuge
Hoto: AFP/Getty Images

Majiyar dakarun sojan kasar Ukraine ta bayyana cewa sojoji 568 ne suka mutu cikin watanni 4 na fadan da suke yi da 'yan aware dake samun goyon bayan Rasha, har ila yau akwai kuma wasu maaikata 2,120 da suka sami raunika kamar yadda Andriy Lysenko mai magana da yawun jami'an tsaron ya bayyana. Wannan adadi na zuwane a daidai lokacin da wadannan dakaru ke kokarin ganin sun kawar da mayakan sakai, a rikicin da Kwamitin bada agajin kasa da kasa na Red Cross yace na iya rikida ya zama yakin basasa.

A cewar Lysenko cikin kasa da sao'i 24 sojojin gwamnati 6 suka mutu a lokacin da suke kara tunkarar biranen Donetsk da Lugansk inda ayyukan 'yan awaren yafi kamari.

Ita kuwa MDD bayyana wa tayi cewa sama da mutane 1,300 ne suka halaka tun bayan rikicin da aka fara a tsakiyar watan Aprilu, fiye da mutane 285,000 kuma suka kauracewa muhallansu .

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo