Dakarun Iran sun shirya don murkushe boren adawa da gwamnati
January 4, 2018Kafafan yada labarun kasar Iran sun ruwaito babban kwamandan sojojin Iran din na cewa dakarunsa sun shirya tsaf don murkushe boren da ake yi na nuna adawa da gwamnati.
A halin da ake ciki 'yar kasar ta Iran da ta taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel, wadda kuma ke zaman hijira a ketare, Shirin Ebadi ta yi kira ga 'yan kasar da su ci gaba da zanga-zanga. Ebadi dai na daya daga cikin lauyoyin kasar masu fafatukar kare hakkin dan Adam.
Boren adawa da gwamnatin ta Iran, a wannan karon shi ne mafi muni tun shekarar 2009. An faro ne don nuna takaici dangane da tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.
Kawo yanzu mutum 21 suka rasa rayukansu, kana an kame wasu daruruwa. An girke dakarun rundunar juyin juya hali a larduna uku a kokarin shawo kan boren.