1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Ukraine sun doshi gabashin kasar

April 15, 2014

Shugaban kasa, na riko a Ukraine mai samun goyon bayan kasashen yamma ya zargi Rasha da kokarin ingiza 'yan awaren da ke yankin kudu maso gabashin kasar

https://p.dw.com/p/1BiLV
Ostukraine Krise ukrainische Armee nahe Slawjansk 14.04.2014
Hoto: picture-alliance/ITAR-TASS

Gwamnatin Ukraine ta yi kira da a dauki matakin soji kan 'yan awaren dake tarzoma a yankin gabashin kasar, shugaban rikon kwaryar kasar Olexsandr Turchynuv ya bayyanawa yan majalisa a birnin Kiev cewa za a dauki wannan mataki ne domin kare al'umma daga 'yan ta'adda wadanda ke neman tayar da zaune tsaye.

Bisa bayanan da shugaban tsaron kasar Andrej Parubi ya bayar, a yanzu haka, runduna ta farko tana bisa hanyar zuwa yankin gabashin, inda 'yan awaren masu makamai suka kama mahimman ofisoshin gwamnati.

Sai dai ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya gargadi Ukraine da ta guji daukar matakin da zai dada ruruta wutar rikicin tun kafin su zauna kan teburin tattaunawar da ake sa ran gudanarwa ranar alhamis a birnin Geneva, karkashin jagorancin Turai da Amirka.

Wannan na zuwa ne bayan da Shugaba Obama na Amirka da Vladimir Putin na Rasha suka tattauna ta wayar tarho, ba tare da sun cimma wani tudun dafawa ba domin Putin ya karyata duk wani zargin cewa da hannunsa a rikicin gabashin Ukraine.

A yanzu haka dai ministocin kula da harkokin wajen kasashen Turai sun jinkirta fadada takunkumin da suka kakabawa Rasha, da fatan cewa tattaunawar ta ranar alhamis, da Turai da Amirka za su jagoranta, zai kawo karshen tankiyar dake tsakanin bangarorin.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu