Dakatar da gidan talbijin na Afrique Media a Kamaru
August 7, 2015Sanarwa da hukumar ta fitar, na cewa shi wannan gidan talbijin na Afrique Media ya zargi kasashen Faransa da Amirka da laifin tallafawa kungiyar Boko Haram, abun da hukumar ta CNC ta ce labari ne wanda babu wani tabbaci a cikinsa, kuma yana iya saka 'yan wadannan kasashe da ke kasashen waje cikin hadari.
A watannin baya-bayannan dai gidan talbijin din ya yi ta gayyato mutanen da suka hada da malaman jami'o'i, da ma kungiyoyin fararan hulla, wadanda cikin mahawara suka yi ta zargin kasashen na Faransa da kuma Amirka da tallafawa kungiyar ta Boko Haram, inda sanarwa ta Hukumar sadarwar ta kasar ta Kamarun ta ce batu na shaci fadi da ake yinsa cikin Yaounde ba tare da wani tabbaci ba.
Tun dai a ranar hudu ga watan Yunin da ya gabata ne hukumar ta yi kashedi wa wannan gidan tabijin, amma kuma sai yanzu mataki ya biyo baya, inda kuma aka dakatar da masu gabatar da wannan shiri na tsawon watanni shidda.