1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakatar da tashar Wazobia a Kano

February 23, 2013

Dakatar da shirye shiryen wannan rediyo na da nasaba da sukar shirin ringakafin shan inna da ta yi. An tuhumi biyu daga cikin ma'aikatan a da laifin tunzura jama'a ga yin bore.

https://p.dw.com/p/17kf6
Hoto: Fotolia/Serggod

Hukumomin Tarayyar Najeriya sun dakatar da lasisin tashar rediyo ta Wazobia sakamakon sukar shirin allurar rigakafin shan inna da ta yi, jim kadan kafin harin da aka kai a cibiyoyin Polio a arewacin kasar. Daya daga cikin shirye shiryen wannan tashar ya danganta allurar da ake digawa yara a baki domin kare su daga cutar Polio da wata manakisa ta "turawan yamma" domin murkushe musulmi a doron kasa. Mutane goma ne dai suka rasa rayukansu a wasu jerin hare hare da aka kaddamar a cibiyoyin rigakafin shan inna a Kano.

An tuhumi biyu daga cikin ma'aikatan Wazobia da kuma malamin da suka yi hira da shi da laifin tunzura jama'a ga yin bore da kuma sauran laifukan da ke da nasaba da hare-haren da aka kai. Sai dai har yanzu babu wasu kwararan shaidu da ke nuna cewa suna da hannu a wannan aika aika. Tsohon shugaban wannan tasha Sanusi kankarofi da ya yi murabus domin nuna goyon baya ga ma'aikatansa ya baiyana wa kanfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa tasharsu ba ta niyar yin kafar ungula ga shirin rigakafin Polio.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi