1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murna na neman komawa ciki a yaki da cutar AIDS

Daniel Pelz LMJ/MNA
December 1, 2020

Tsawon shekaru, an samu nasarar dakile tasirin kwayar cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS ko kuma SIDA a kasashen Afirka da dama, godiya ga magungunan da ke taimakawa rayuwar masu dauke da wannan cuta.

https://p.dw.com/p/3m4q4
Ba da shawara cikin kayan kariya: Wadannan takunkuman ba su da alaka da HIV sai dai corona
Ba da shawara cikin kayan kariya: Wadannan takunkuman ba su da alaka da HIV sai dai coronaHoto: Bram Janssen/AP/picture alliance

Amma wani hanzari ba gudu ba, ana iya cewa murna na neman komawa ciki, musamman ma a wannan lokaci da ake fama da annobar coronavirus. A daidai lokacin da ake gudanar da bikin ranar yaki da kwayar cutar ta HIV/AIDS ko kuma SIDA.

Masana sun yi ittikafin cewa sakamakon bullar annobar ta coronavirus da ta addabi duniya, sama da mutane dubu 290 ka iya kamuwa da cutar ta HIV/AIDS ko kuma SIDA yayin da kimanin wasu dubu 148 ka iya rasa rayukansu, duk dai sanadiyyar cutar mai karya garkuwar jiki.

Karin bayani:COVID-19 da yaki da cutar HIV/AIDs ko SIDA

Gilbert Tenes likita ne da ke kula da masu fama da cuta mai karya garkuwar jikin a kasar Kamaru, ya shaida wa DW cewa aikinsa ya kara zama mai matukar wahala:

"COVID-19 ta zo ne ta kara ta'azzara al'amura in har ana batu ne na cuta mai karya garkuwar jiki, wato HIV/AIDS ko kuma SIDA. Marasa lafiya na dari-darin zuwa asibiti. Muna bukatar marasa lafiyar su zo asibiti domin kwantar musu da hankali da kuma ba su magunguna da sauran taimakon da suke bukata. Hakan ce ta sanya muka fito da wani tsari, inda muke shiga cikin al'ummomi domin taimaka wa marasa lafiyar da ba za su iya zuwa asibiti ba."

In har masu dauke da kwayar cutar ta HIV/AIDS ko kuma SIDA na samun magani, rayuwarsu ka iya yin tsawo. Likitoci a Afirka ta Kudu sun koka kan yadda al'umma ke mutuwa a asibitoci, abin da ke sanya wasu fargabar zuwa asibiti neman maganin.

Corona ta kara damuwa da rashin tabbas ga wannan dan Kenya mai fama da cutar HIV
Corona ta kara damuwa da rashin tabbas ga wannan dan Kenya mai fama da cutar HIVHoto: Donwilson Odhiambo/ZUMA/picture alliance

An dai samu mace-mace ba adadi sanadiyyar COVID-19 da tarin fuka da kuma cuta mai karya garkuwar jiki. Masu dauke da cututtuka kamar tarin fuka da HIV/AIDS ko kuma SIDA da ma sauran cututtuka da suka samu sauki da ba su samu damar sake komawa asibiti domin sake dubar lafiyarsu kamar yadda aka saba ba na mutuwa, saboda sun garzaya asibitin a makare sakamkon matsaloli da dama da suka hadar da dokar kulle sakamakon annobar coronavirus.

Karin bayani: Maganin HIV na kawo sauki ga masu Corona

A cewar Winnie Byanyima daraktar Hukumar Kula da Cuta mai Karya Garkuwar Jiki ta Majalisar Dinkin Duniya UNAIDS, an samu raguwar masu kamuwa da cutar da kaso daya bisa uku a shekaru shidan da suka gabata a yankin gabashi da kudancin Afirka, kana an samu raguwar wadanda cutar ke halakawa da kaso 40 cikin 100. Sai dai Byanyima ta ce:

"Akwai gagarumin ci-gaba a yankunan da suka zama cibiyar wannan cuta a gabashi da kudancin Afirka. An samu raguwar masu kamuwa da cutar da ma masu mutuwa a sakamakonta. Kasashe kamar Botswana sun cimma dukkan fatan da suka saka a gaba. Abin takaici mun samu rahotanni da ke nunar da cewa a kasashe da dama lokacin dokar kulle da aka rufe makarantu yara na gida, na samu cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar fyade. Fyaden da ake wa mata da yara mata ne ya fi zama sanadin yaduwar cutar musamman a yankin Kudu da Saharar Afirka."

A hannu guda kuma, annobar coronavirus, ta kara sanya fannin kiwon lafiya a nahiyar Afirka cikin tsaka mai wuya. Tun kafin bullar annobar, akwai karancin likitoci da jami'an kiwon lafiya a kasashen Afirka da dama. A yanzu tilas su kula da marasa lafiya ba wai wadanda ke fama da kwayar cutar HIV/AIDS ko SIDA kawwai ba, har ma da masu fama da annobar COVID-19. Hakan kuma na nufin za su yi kasada da rayukansu sakamkon karancin kayan aiki da ake fama da su a mafiya yawan asibitocin kasashen nahiyar, abin da ya sanya ma'aikatan lafiya da dama suka kamu da cutar tare kuma da rasa rayukansu.

An dauki wannan hoto na magungunan HIV ga masu jinya a Zimbabuwe gabanin bullar corona
An dauki wannan hoto na magungunan HIV ga masu jinya a Zimbabuwe gabanin bullar coronaHoto: Jekesai NJIKIZANA/AFP

Masu fafutukar ganin an kawo karshen cutar ta HIV/AIDS ko SIDA a Afirka dai na korafin karancin kudi, kamar yadda Awa Fany da ke aiki da wani shiri na yaki da HIV/AIDS ko SIDA a Cocin Baptist a Kamaru ta  yi karin hasske a wata hira da tashar DW tana mai cewa an samu karancin kudi, kasancewar wadanda ke taimakawa a yanzu sun juya akalar taimakonsu zuwa ga annobar COVID-19. Ta kara da cewa suna tunanin yadda za su raba agajin wajen kulawa da yara masu dauke da kwayar cutar HIV/AIDs ko kuma SIDA da kuma wadanda suka kamu da cutar COVID-19."

Karin bayani:Kalubalen masu AIDs ko SIDA a Najeriya

Matsalar karancin kudin dai ba wai ta shafi Cocin Baptist ta Kamaru kadai ba ne, har ma da Asusun Yaki da Kwayar Cutar HIV/AIDS ko SIDA a Afirka, kamar yadda daraktan asusun Peter Sands ke cewa:

"Babban tashin hankalina a wannan yanayin shi ne, masu bayar da tallafin kudi a duniya baki daya, sun tsinci kansu wajen kawo karshen annobar COVID-19, kuma da wadannan adadin kudi, zai kasance ba za mu iya yakar cututtuka hudu a lokaci guda ba, za kuma a samu karin mutane da dama da za su mutu."

Yanzu dai shawara ta ragewa gwamnatocin kasashen duniya. Wata kungiyar Kula da ci-gaban kasashe a duniya mai suna ONE, ta nunar da cewa ana bukatar kimanin sama da dalar Amirka miliyan biyar, wajen rage tasirin annobar coronavirus a kan masu dauke da cutar HIV/AIDS ko SIDA. Sai dai kuma gwamnatocin na fama da matsalar tattalin arziki da annobar ta coronavirus ta janyo.