Daliba ta kashe malamarta da wata daliba da bindiga a Amurka
December 17, 2024Wata daliba mai shekaru 15 dauke da bindiga ta harbe malamarta da wata daliba har lahira a Amurka, sannan kuma ta raunata wasu guda shida, bayan bude musu wuta a makarantarsu ta Christian school da ke jihar Wisconsin.
Karin bayani:Trump ya sake tsallake rijiya da baya a yunkurin halaka shi
Rundunar 'yan sandan Amurka ta ce dalibar da ta yi harbin mai suna Natalie Rupnow, ta mutu a lokacin ake kan hanyar kai ta asibiti, sakamakon harbin da ta yi wa kanta da kanta.
Karin bayani:Mai yunkurin halaka Donald Trump ya gurfana a kotu
Tuni dai shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya nuna kaduwarsa da faruwar lamarin, yana mai kiran majalisar dokokin kasar ta hanzarta amincewa da yi wa dokar mallakar bindiga gyara, don dakile yawaitar kisan da ake samu a dalilin hakan.