Dalilai 10 na zuwa ziyara Isra'ila
Shekaru 75 ke nan da aka kafa Isra'ila, wato rana 14 ga watan Mayu na 1948. Wuri ne da ke da ban sha'awa ga masu yawon bude ido, musamman a bangaren tarihi da al'adu da kuma addinai.
Cibiyar Yad Vashem
Cibiyar tunawa da kisan kare dangi da aka yi wa Yahudawa ta Yad Vashem da ke Birnin Kudus, ta kasance guda daga cikin wuraren tarihi da ake yawan ziyarta a Isra'ila. An yi ta ne saboda tunawa da Yahudawa miliyan shida da 'yan Nazi suka yi wa kisan gilla. Bayan karnonin da aka kwashe ana nuna musu danniya, Isra'ila ta zama gida ga Yahudawan duniya baki daya.
Dutsen Haikali da ke Birnin Kudus
Isra'ila na da mabambantan al'ummomi, wadanda suke da al'adu da kuma addinai dabam-dabam. Duk shekara, sama da mutane miliyan hudu ne suke kai ziyara Isra'ila. Wani waje da ya yi fice wajen karbar baki shi ne, Dutsen Haikali da ke Birnin Kudus da ya shafe shekaru 2,000. Yana da matukar tasiri a wajen Yahudawa da Kitristoci da kuma Musulmai.
Dutsen Haikali da Masallacin Al-Aqsa
Ga Musulmi, Dutsen Haikali na zaman waje na uku mafi tsarki bayan Maka da Madina. An yi amannar cewa daga Masallacin da ke jikin Dutsen Haikali ne Annabi Mohammed ya yi isra'i da mi'iraji. Shi ma Masallacin Al-Aqsa (da ke jikin wannan hoto), wanda ke daukar masu bauta 5,000 a kan Dutsen na Haikali yake.
Bangon wajen bautar Yahudawa
Romawa sun tarwatsa wajen bautar Yahudawa da a baya ke cikin Masallacin Al-Aqsa, a shekaru na 70 Miladiyya. Bangon Yamma na wajen bautar da ake kira da "Wailing Wall," shi ne ya yi saura daga wajen bautar da aka rusa. Yana da fadin mita 48, yayin da tsawonsa ya kasance mita 18. Ana ware wadanda suka zo bauta nan wajen, wato mata dabam maza dabam.
Mujami'ar Holy Sepulcher
Ga Kiristoci ma Dutsen Haikali na da muhimmanci, kasancewar Annabi Isa ya yi abubuwa da dama a wajen kamar yadda yake a New Testament. Za ma a iya cewa ya fi muhimmanci ga Kiristoci, sai dai kuma a Birnin Kudus Mujami'ar Holy Sepulcher na da muhimmanci da a al'adar Kiristocin a nan ne aka gicciye Annabi Isa.
Lambun Haifa
Tabbas akwai manyan wuraren tari a wajen Birnin Kudus, kuma daga cikinsu akwai Lambun Haifa. Ya kasance kushewar Bab, wato an mallaka shi ne ga wanda ya samar da Addinin Babi ko Baha'i. Wurin na zaman guda daga cikin wuraren tarihi da Hukumar Kula da Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta ayyana a matsayin wuraren tarihi na duniya.
Kogin Jordan
Kowa na tunanin, ya mutum zai ji idan ya zama ba shi da nauyi? Ba matsala, garzaya Kogin Jordan, tafkin da ruwansa ke da dandanon gishiri mai yawa. Saboda yawan dandanon gishirinsa da ya kai kusan ribi 10 na dandanon gishirin da ke cikin teku, linkaya a cikinsa tamkar an saka roba cikin ruwa. Baya ga haka, wanka a cikin ruwan mai gishiri na inganta lafiyar fatar dan Adam.
Wuraren shakatawa
Da dama cikin wuraren shakatawa a Isra'ila, na da matukar muhimmanci wajen gano yanayinta da tarihinta. Ga misali a wajen shakatawa na En Gedi Nature Reserve, za ka samu "Wadi David" da wurare masu yawa da ruwa ke kwarara. Ko kuma a wurin shakatawa na Masada, inda za ka samu tsauni da kuma birbidin Fadar Romawa.
Hamadar Negev
Kaso kusan 60 cikin 100 na Isra'ila na Hamadar Negev, sai dai kimanin kaso 10 cikin 100 na al'ummar Isra'ila kacal ne, suka mallaki wannan gagarumin waje da ke kudanci. Masu yawon bude idanu na zuwa domin ahwan tsauni a nan, tare da samun yanayi mai kyau. Sai dai tilas a kiyaye, wajen na da tsananin zafi, sai mutum ya kare kansa daga zafin rana ya kuma sha ruwa mai yawa.
Birnin Tel Aviv
Birnin Tel Aviv ya kasance cibiyar tattalin arziki da al'adu na Isra'ila. A nan za ka iya shakatawa a gabar ruwa, tare da kallon gine-gine masu kayatarwa. Kana iya zagayawa cikin kasuwannin birnin da hantsi, ko ka debi girki a gidanjen sayar da abinci kana ka shakata cikin dare.