1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalilin talauci na manoman Koko a Afirka

Abdullahi Tanko Bala
April 23, 2024

Farashin Koko a duniya ya yi tashin gwauron zabi a watan Afrilu wanda aka dade ba a ga irinsa ba, sai dai manoman Kokon a Afirka na fama da talauci a kasashe kamar Ghana

https://p.dw.com/p/4f6LX
Ghana Asikasu | Kakaoplantage
Hoto: cristina Aldehuela/AFP/Getty Images

Tsarin yadda ake sanya farashin musamman a yankunan da ake noma Koko ya jefa manoman cikin kangin rayuwa da rashin kyakkyawar makoma.

Hukumar kula da kasuwancin kokon a Ghana wadda ke sa ido kan harkokin, ta sanar a baya bayan nan cewa za ta kara yawan abin da ta ke biyan manoman kokon a kan wane ton guda. Ta ce yin hakan ya zama wajibi domin bunkasa kudin shiga ga manoman kokon.

Galibi ana kayyade farashin kokon ne a kasuwannin biranen New York da London bisa yawaitarsa da kuma bukatarsa a kasuwannin duniya.