1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambaruwar siyasa na kara kamari a Isra'ila

Mahmud Yaya Azare
March 27, 2023

Dambaruwar siyasa a Isra'ila ya dauki sabon salo bayan da Firaiminista Benjamin Netenyahu ya kori ministan tsaron kasar da ke adawa da shirinsa na gyaran fuskar ga bangaren shari'a

https://p.dw.com/p/4PJhk
Israel Protest gegen die Justizreform
Hoto: Ilan Rosenberg/REUTERS

 A wani yanayi mai kama da zanga zangar neman yin juyin juya hali da ta barke a kasashen Larabawa shekaru 12 da suka gabata, dubban jama'a a garuruwan Isra'ila sun yi gangami inda suke kira ga firaim minista Netanyahu da yayi murabus, bayan kwashe makwanni 12 ana zanga zangar adawa da kudirin dokar da ya gabatar a majalisa don yin garambawul ga tsarin shari'ar kasar da ake zargin yana yi ne da nufin kare kansa daga zarge zargen cin hanci da rashawa. Wani daga cikin 'yan zanga zangar ya yi tsoakci.

"Ya ce mun fito ne don kare tafarkin dimukuradiyya tare da ganin bayan mulkin kama karya na Benjamin Netanyahu wanda baya kaunar cigaban dimukuradiya."

   Jami'an tsaro sun yi amfani da ruwan zafi da hayaki mai sanya kwalla don tarwatsa masu zanga zangar da suka jawo komai ya tsaya cik a manyan biranen kasar: Masu zanga zangar dai sun lashi takobin ci gaba da fafutuka har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi:

Israila | Benjamin Netanjahu a majalisar dokoki ta Knesset
Israila | Benjamin Netanjahu a majalisar dokoki ta KnessetHoto: Ohad Zwigenberg/AP Photo/picture alliance

"Dole ne mu ci gaba da fafutukar kare hakkokinmu na yan kasa, tun da Netanyahu ya dage sai ya canja tsarin shari'a da nufin kare kansa daga barnan da ya tafka don ya kafa tsarin mulki na kama karya."

    Hakan dai na zuwa ne,yan sa,oi bayan da Netenyahun ya sanar da sallamar ministan tsaron kasar, Yoav Gallant, wanda ya zarga da yiwa gwamnatinsa zagon kasa,bayan da ministan  ya nemishi da ya janye dokar garambawul a tsarin sharia,ar kasar da yace tana barazana ga dunkulewar kasar ta Isra,ila:

  "Don tabbatar da tsaron Isra'ila da kare rayukan yayanmu manyan gobe, ya zama wajibi a dakatar da wannan gyaran dokar da ta kawo rarrabuwar kawuna, lamarin da ke barazana ga kasarmu."

Zanga zangar adawa da kwaskwarima ga bangaren shari'a a Israila
Zanga zangar adawa da kwaskwarima ga bangaren shari'a a IsrailaHoto: Ariel Schalit/AP Photo/picture alliance

 A wani labarin kuma karamin jakadan Isra'ila a birnin New York, Asaf Zamir shi ma ya sanar da yin murabus, bayan korar ministan tsaron na Isra'ila. A yayin da kawancen gwamnatin da Netanyahun ke jagoranta ke tangal tangal jam'iyyu masu matsanancin ra'ayi sun yi barazanar gurfanar da Netanyahun gaban kuliya kan cin amanar kasa, muddin ya mika wuya ga kiraye kirayen wadanda suka kira makiya kasar Yahudawa na jingine aiki koma soke sabuwar dokar garambawul ga tsarin shari'ar kasar da suke cewa zai kawo karshen katsalandan da tarnakin da kotuna ke yi wa shirinsu na mayar da kasar Isra'ila ta Yahudawa zalla da bawa larabawa damar kalubantarsu a yayin da masu adawa da dokar ke cewa,an tsarata ne don kare firaiminista Netanyahu daga fuskantar shari'a ko tsigewa komai irin almundahanar da ya aikata.