1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwa kan dokar tsawaita wa'adin kananan hukumomi a Nijar

Mahaman Kanta RGB
August 16, 2017

Gwamnatin Nijar ta sanar da tsawaita wa'adin mulkin shugabannin kananan hukumomi da watanni 6, bayan cikar wa'adin mulkinsu ba tare da shirya sabon zabe ba lamarin da yanzu ya haifar da ce-ce-ku-ce.

https://p.dw.com/p/2iMsq
Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Gwamnatin Nijar ta sanar da tsawaita wa'adin mulkin shugabannin kananan hukumomi da watanni shida, bayan cikar wa'adin mulkinsu ba tare da shirya sabon zabe ba, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsare da wasu daga cikin magadan gari da ake zargi da almundahana.

A sha biyun daren wannan rana ta Laraba ce wa'adin wakillan majalisun kananan hukumomi da shugabanninsu na birnin Yamai da kewaye ke karewa. Batun ware Yamai da sauran garuruwan da ke kewaye da birnin shi ne abinda ya daurewa jama'a kai, lamarin ya sa masana kan dokokin tsarin mulkin kasar yin fashin baki a kai. Akwai wadanda ke ganin dokar karkasa yankunan ta na kawo bambamcin a kan kananan hukumomi ko manyan birane muddin ya kasance tsarin yanayinsu ya banbanta, masana na ci gaba da tafka mahawara a kan wannan kudiri mai cike da sarkakkiya.