1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar rikicin kuɗin Girka

June 27, 2011

Ƙasashen Turai na cikin shirin ko ta kwana dangane da rikicin kuɗin Girka ko da za ta gaza biyan bashin da ake binta.

https://p.dw.com/p/11jyk
Tambarin kuɗin EuroHoto: Fotolia/interlight

Ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble ya ce ƙasashen turai masu amfani da takardun kuɗin bai ɗaya na euro suna zaune cikin shirin ko ta kwana dangane da rikicin kuɗin Girka, ganin cewa mai yiwuwa ba zata iya biyan basussukan da ƙasashen suka bata ba. Schäuble ya bayyana haka ne wa wata jaridar lahadi na nan Jamus wato The Bild am Sonntag, inda kuma ya ƙara da cewa da shi da sauran takwarorin sa na EU na sa ran Girka ta gabatar da shirinta na matakan tsuke bakin aljihu na kimanin euro milliyan dubu 28 a wannan makon, domin idan ba haka ba, ƙungiyar EU da asusun bada lamuni na duniya wato IM F ba zasu sakan mata kason na euro dubu milliyan 110n da suka alƙawarta mata a bara ba. Mataimakin Frime Ministan Girkan, Theodoros Pangolos ya faɗawa wata jaridar Spain mai suna El Mundo cewa shawarar Girka ta koma amfani da takardun kuɗinta na daa wato drachma bata da wata a'ala ga halin da ake ciki yanzu, kuma yin hakan zai haddasa tarzoma da zanga-zangar da zai yi tasiri akan tattalin arziƙin Turai gaba ɗaya. Manyan ƙungiyoyin ƙwadagon Girkan dai sun ce zasu gudanar da yajin aiki na tsawon kwanaki biyu daga gobe talata.

Mawallafiya: Pinadɗo Abdu
Edita: Abdullahi Tanko Bala