1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baiyanar sojojin Turai a Kwango

Simone Schlindwein ZMA
January 20, 2023

Bullar wasu sojoji daga gabashin Turai a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango mai fama da rikici, ta sanya damuwa a zukatan jami'an diplomasiyyar yammaci.

https://p.dw.com/p/4MUkE
Mayakan tawayen KwangoHoto: GLODY MURHABAZI/AFP via Getty Images

Duk da cewa tana ci gaba da musantawa, akwai jita-jita mai karfi da ke zargin Kinshasa da yin hayar sojojin Wagner daga Rasha. An dai kwashe kusan mako guda ana rade-radin ganin dakarun na gabashin Turai a garin Goma, kimanin kilomita 30 da kudancin wajen da a yanzu ya zama filin daga. 

An dai hangi jami'an tsaro fararen fata sanye da kayan sarki a Otel din Mbiza da ke Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, wanda a kan yi amfani da shi wajen sauke 'yan kasuwa da kuma bakin gwamnati. Wani dan jaridar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidar da cewa, sojojin na dauke da makamai kuma an tsaurara tsaro a kofar shiga otel din, inda jami'a na musamman da ke kare lafiyar shugaban kasa ke gadin wurin. Josué wani makwabcin filin saukar jiragen sama na kasa da kasar da ke Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ne, ga kuma abin da yake cewa:

DR Kongo Ein M23-Rebellen
Mayakan M23 a KwangoHoto: GLODY MURHABAZI/AFP via Getty Images

"Mun ga wasau mutane a filin jiragen saman, sun yi kama da 'yan Rasha ko kuma masu goyon bayanta ko ma 'yan Romaniya. Sai dai har yanzu ba mu samu wani karin bayani ba, amma mutane ne da ba sa cikin rundunonin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa na MONUSCO ko EAC. Da idanuna na ga kusan mutane 100, wasu na sanye da kaki wasu kuma babu. Sai dai tabbas suna dauke da makamai, ba sa yawo don haka ba a ganinsu a cikin gari."

Rikici dai ya barke a farkon shekarar da ta gabata, bayan da 'yan tawayen M223 suka kwace yankuna da dama da ke kan iyakokin kasar da Ruwanda da kuma Yuganda. Jami'an tsaron Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango dai na fuskantar gagarumar asara, abin da ya haifar da jita-jitar cewa gwamnati ta hayo sojojin hayar Wagner na Rasha domin taimaka mata bayan ganin fararen fatar jami'an tsaron a otel din Mbiza. Sai dai kakakgin gwamnatin Kwangon da ya kasasnce ministan sadarwa da yada labarai Patrick Muyaya ya bayyana cewa:

"Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na da ikon ta tsara yadda za ta kare kanta, ga misali muna da jiragen yaki na Suchoi da jami'anmu ba za su iya aiki da shi ba sai da muka hayo sojojin Faransa su ba su horo. Hakan ba yana nufin mun yi wo hayar sojojin wata kasa domin su yi yaki a kasarmu ba, sam ba haka ba ne."

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar da cewa, akwai kimanin injiniyoyi da sauran masu kula da lafiyar jiragen sama kimanin 40 a filin saukar jiragen saman na Goma. Daga cikinsu akwai 'yan Bulgariya da Jijiya da Belaru da ke da masaniya kan jiragen yakin Rasha. Reagan Miviri mai bincike kan dalilan rikici a kungiyar Congo Study Group  GEC, ta nunar da cewa:

Demokratische Republik Kongo | Soldaten der EACRF und M23 Rebellen in Kibumba
Yankin gabashin Kwango mai fama da rikiciHoto: GLODY MURHABAZI/AFP/Getty Images

"Tabbas akwai wasu jami'an kasashen waje, musamman a Goma da aka cewa za su bai wa sojojin Kwango horo ne. Musamman a fannin bai wa sojojin sama da matuka jirgin saman yaki horo, muna batun 'yan Romaniya da kuma wasu kasashen gabashin Turai."

Tun dai a shekarar da ta gabata ne, Kinshasa ta fara karfafa huldarta da Moscow. Ko da a watan Agustan bara ma, ministan tsaron Kwangon Gilbert Kabanda ya halarci taro kan tsaro da Rashan ta shirya. Moscown dai ta yi wa Kwango alkawarin tallafin kayan yaki da suka hadar da tankoki da jirage.