1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Wani dan Britaniya ya mutu a fagen daga

Ramatu Garba Baba
April 28, 2022

Wani dan kasar Britaniya da ya shiga yakin Rasha don taimaka wa Ukraine ya mutu a wannan Alhamis a fagen daga. Akwai yiyuwar ma'aurata ne da suka shiga yakin.

https://p.dw.com/p/4AaE1
Ukraine | Exhumierung eines Massengrabs in Mykulytschi
Hoto: Emilio Morenatti/AP/picture alliance

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Ukraine ce ta soma fitar da sanarwar, inda a ciki ta fadi mutuwar wani dan kasar Britaniya da kuma wata da ba a gani ba tun bayan wani gumurzu da dakarun Rasha, suna daga cikin wadanda suka shiga kasar don taya Ukraine fada da Rasha.

Kafofin yada labaran Birtaniya kuwa, sun ce, akwai yiyuwar ma'aurata ne da suka shiga yakin amma ba a tabbatar da hakan ba. Tuni Ofishin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya soma tuntubar danginsu a yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken gano wacce ba a gani ba.