1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMasar

Dan sanda ya bindige 'yan Isra'ila biyu a Masar

October 8, 2023

Wani jami'in 'yan sanda a Masar ya bindige wasu 'yan kasar Isra'ila biyu masu yawon buda ido da kuma jagoransu dan kasar Masar a birnin Alexandrie da ke gabar Tekun kasar.

https://p.dw.com/p/4XGKq
Dan sanda ya bindige 'yan Isra'ila biyu a Masar Hoto: Xinhua/IMAGO

Wannan lamari da ba a cika ganin irisa ba na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar 'yan ta'adda ta Hamas da ke da iko da Zirin Gaza na yankin Falasdinu.

Karin bayani: Mutane da dama sun halaka a Isra'ila da Zirin Gaza

Bayan ta tabbatar da aukuwar lamarin, ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta sanar da daukar matakin kwashe ragowar 'yan Kasarta da ke yawon buda a Masar domin mayar da su gida.

Sai dai har kawo yanzu gwamnati Masar ba ta fidda sanarwa kan wannan lamarin ba, to amma gidan talabijin din kasar ya ruwaito cewa an kama dan sandan take-yanke bayan ya hallaka mutanen biyu tare da jikkata wani mutun guda dukanninsu 'yan Isra'ila.