1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

'Dan wasan Spain Lamine Yamal ya kafa tarihi a gasar Euro

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 10, 2024

Yamal ya zura kwallo a gasar cin kofin kasashen turai Euro, a wasan da kasarsa ta doke Faransa da ci 2-1

https://p.dw.com/p/4i5OM
Hoto: Leonhard Simon/REUTERS

'Dan wasan kasar Spain Lamine Yamal mai shekau 16, ya kafa tarihin zama 'dan wasa mafi karancin shekaru da ya zura kwallo a gasar cin kofin kasashen nahiyar turai Euro, bayan da ya jefa kwallo a wasan da kasarsa ta doke Faransa da ci 2-1, a zagayen dab da na karshe a daren Talata a birnin Munich, wanda ya bai wa Spain din damar zuwa wasan karshe na gasar da ke gudana a Jamus.

Karin bayani:

Tun farko Randal Kolo Muani ne ya fara jefa wa Faransa kwallo, sannan Lamine Yamal farke wa Spain, yayin da daga bisani Dani Olmo ya zura wa Spain din ta biyu, da ta ba ta nasara.

Karin bayani:Wasannin quater finals a gasar Euro 2024

Da karfe 9 na daren Laraba agogon Jamus, Ingila za ta kara da Holland, domin neman cancantar buga wasan karshe da Spain.

A ranar 14 ga watan Yulin nan ne dai za a buga wasan karshe na gasar ta Euro 2024.