1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta yi barazanar bude kan iyakokinta

Zainab Mohammed Abubakar
March 1, 2020

Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya yi barazanar barin dubban dubatan 'yan gudun hijira su kwarara zuwa cikin Turai, bayan kashe gomman dakarun kasar a cikin Siriya.

https://p.dw.com/p/3YgD5
Türkei Ausschreitungen am Grenzübergang Pazarkule zu Griechenland
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Gurel

Turkiyya ta yi ikirarin bude kan iyakokinta da kasashen Turai ga 'yan gudun hijira dubu 75. Zuwa safiyar wannan Lahadin dai, 'yan gudun hijira sama da dubu 76 ne, suka cimma tsallake kan iyakar Turan ta gundumar Edirne, a cewar ministan harkokin cikin gida Suleyman Soylu.

A wannan yanki, a kwai mashigar Girka da Bulgaria. Da farko dai kasashen biyu basu sanar da kwararan baki 'yan gudun hijirar ba, inda gwamnatin Sofia ta ce, babu dan gudun hijirar da ya keta kan iyakarta ba bisa ka'ida ba.

Framinstan Bulgaria Boyko Borisov na shirin ganawa da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya a gobe Litinin, domin tattauna rikicin Siriya da 'yan gudun hijirar da suka yi cincirindo a kan iyakokin kasashen a yanzu haka.