1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantaka na kara tsami tsakanin Girka da Turkiyya

Zulaiha Abubakar MNA
April 3, 2018

Kasar Girka ta ja hankalin mahukuntan kasar Turkiyya a kan su saki sojojinta da suka tsare tun farkon watan Maris a cikin wata sanarwa da Firaministan Girka ya raba wa manema labarai.

https://p.dw.com/p/2vQ4L
Athen Präsident Erdogan Türkei besucht Griechenland
Hoto: Reuters/C. Baltas

Sanarwar ta kara da cewa sojojin na Girka sun tsallaka kasar Turkiyya ne bisa kuskure yayin da suke bin sawun wasu 'yan gudun hijira duk kuwa da cewar kasar Turkiyya na zargin sojojin da shigar mata kasa ba bisa ka'ida ba da kuma ayyukan leken asiri.

Firaministan ya kara da cewar yana sa ran Shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiyya ya yi adalci wajen sakin wadannan sojoji musamman in aka yi la'akari da yadda a baya kasar ta Girka ta mayar da wasu sojojin Turkiyya da suka shigar mata kasa ta barauniyar hanya.

Dangantaka ta fara tsami tsakanin kasashen biyu kan batutuwan da suka shafi kasar Cyprus.