Dangantaka takanin Jamus da Turkiyya na kara yin tsami
July 20, 2017Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana furucin da ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya yi na sauya alkiblar manufar siyasar Jamus dangane da kasar Turkiyya da cewa abu ne muhimmi da ya zama wajibi a dauka. Da farko dai a martanin da ya mayar dangane da kame wani Bajamushe mai faftukar kare hakkin dan Adam wato Peter Steudtner da wasu mutane da Turkiyya ta yi, ministan harkokin waje Gabriel ya ce za a tsaurara bayanai kan tafiye tafiye zuwa Turkiyya, yana mai cewa ana gallaza wa Jamusawa da ke zuwa Turkiyya, abin da ke jefa su cikin rashin tabbas.
Ya ce: "Har yanzu akwai kyakkyawar hulda tsakanimu da Turkiyya. Muna son kasar ta zama daya daga cikin kasashen yamma. Amma take-taken gwamnatin Turkiyya a yanzu ya sa a dole Jamus za ta yi nazari kan dangantakarta da Turkiyya. Matakin farko da muka dauka shi ne ba da sabbin shawarwari ga Jamusawa da ke kai ziyara Turkiyya."