1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta farfado da dangantakarta da Iran

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 15, 2015

Mataimakin shugabar gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel zai jagoranci wata tawaga ta 'yan kasuwa zuwa Iran domin tattauna batun karfafa kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/1Fz8z
Mataimakin shugabar gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel.
Mataimakin shugabar gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel.Hoto: Getty Images/S. Gallup

Gabriel wanda kuma shi ne ministan tattalin arziki da makamashi na Jamus din zai fara ziyarar ne daga ranar Lahadi 19 ga watan nan na Yuli da muke ciki zuwa Talata 21 ga watan na Yuli. A wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugabar gwamnatin ta Jamus ta mika ga kamafanin dillancin labaran Faransa AFP, ta bayyana cewa Gabriel din zai jagoranci wata karamar tawaga ta wakilan masana'antu da kuma kimiyya ne zuwa Iran din. Wannan sanarwa dai na fitowa ne kwana guda bayan da Iran din ta cimma yarjejeniya kan batun makamashin nukiliyarta da manyan kasashen da ke fada aji a duniya shida. Dama dai dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen Iran da Jamus na da karfi, sai dai ta samu nakasu sakamakon takunkumin karya tattalin arzikin da kasashen duniya suka kakabawa Iran din dangane da batun makamashin nukiliyarta.